Silva bai ji rauni a mukamuki ba

David Silva Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Silva zai buga wasan da Man City za ta yi da Aston Villa ranar Asabar

Likitocin Manchester City sun sanar da cewar David Silver bai ji rauni a mukamukinsa ba a karawar da suka yi da West Ham a Premier.

Dan kwallon West Ham Cheikhou Kouyate ne ya doki fuskar Silva da gwiwar hannunsa, lamarin da ya sa aka cire dan wasan daga fili a kan gadon daukar marasa lafiya.

Rahoto daga binciken da aka yi a asibiti ya tabbatar da cewar dan wasan mai shekaru 29 bai ji mummunan rauni ba kamar yadda aka zata tun farko.

Silva dan kasar Spain zai iya buga wa Manchester City tamaula a gasar Premier da Aston Villa a ranar Asabar mai zuwa.

Manchester City ce ta doke West Ham da ci 2-0 a ranar Lahadi, ta kuma ci gaba da zama a mataki na hudu a teburin Premier da maki 64.