Ribery ba zai buga wasa da FC Porto ba

Frank Ribery Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ribery ya kwashe makwanni shida yana jinyar rauni

Franck Ribery ba zai buga wa Bayern Munich wasan daf da na karshe da FC Porto ba, a gasar cin kofin zakarun Turai karo na biyu a ranar Talaba.

Dan kwallon Faransa, mai shekaru 32, bai buga wasan farko da suka yi a Portugal ba, sakamakon jinya da yake yi, kusan makwanni shida kenan.

Sai dai kuma Bastian Schweinsteiger wanda bai buga karawar wasan farko ba, zai buga wasa na biyu a Jamus.

'Yan wasan Porto Danilo da Alex Sandro ba za su buga fafatawar ba sakamakon dakatar da su da akayi, amma mai tsaron baya Ivan Marcano zai taka leda a karawar.

FC Porto ce ta doke Bayern Munich da ci 3-1 a Porugal a karawar da suka yi a makon jiya.