Munich ta kai wasan daf da karshe a kofin Turai

Bayern Munich
Image caption Munich ta yi fama da rashin manyan 'yan wasanta, sakamakon jinya da suke yi

Bayern Munich ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da ta doke FC Porto da ci 6-1 ranar Talata.

Munich din ta zura kwallaye biyar ne ta hannun Thiago Alcántara da Boateng da Lewandowski wanda ya ci biyu a wasan sai kuma Muller da shi ma ya zura kwallo a raga a karawar.

Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci ne Munich ta ci kwallayen biyar, a inda FC Porto ta ci kwallo daya tilo ta hannun Martinez saura minti 17 a tashi daga wasan.

Porto ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Marcano Sierra jan kati, kuma damar da Munich ta amfana da ita a inda ta ci kwallo ta shida ta hannun Alonso.

Wasan farko da suka fafata a Porugal, FC Porto ce ta doke Munich da ci 3-1.