An sake nada Keshi a matsayin kocin Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Stephen Keshi

An sake nada Stephen Keshi a matsayin kocin tawagar Super Eagles ta Nigeria a karo na uku.

Ya sanya hannu a yarjejeniyar shekaru biyu a ranar Talata tare da hukumar kwallon kasar watau NFF.

A karon farko da aka nada shi, ya jagoranci kasar ta lashe gasar cin kofin Afrika a 2013 amma sai aka soma takun saka tsakaninsa da NFF bayan kamalla gasar cin kofin duniya a Brazil.

Keshi ya ce "Muna bukatar goyon bayan 'yan Nigeria domin ciyar da tawagar 'yan kwallon kasar gaba."

Dan shekaru 53, Keshi kuma ya sanya hannu a takardar yin da'a da biyayya sannan zai yi aiki karkashin wani kwamiti na musamman na NFF.