Nasarawa United ta doke Pillars da ci 2-1

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Site
Image caption An buga wasannin mako na biyar a gasar Premier Nigeria ta bana

Nasarawa United ta samu maki uku a kan Pillars bayan da ta doke ta da ci 2-1 a gasar cin kofin Premier Nigeria wasannin mako na biyar da suka kara ranar Laraba.

Kungiyar Enyimba ta garin Aba ta doke FC Taraba da ci daya mai ban haushi har gida, kuma Mfon Udoh ne ya zura kwallo a ragar.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Heartland ta yi rashin nasara a gida da ci daya mai ban haushi a hannun Abia Warriorrs.

Giwa FC kuwa zazzaga kwallaye hudu da nema ta yi a ragar Akwa United, kuma shi ne wasan da aka fi cin kwallaye a wasan mako na biyar na gasar.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

FC Taraba 0-1 Enyimba Heartland 0-1 Abia Warriors Gabros 2-0 Lobi Stars Giwa 4-0 Akwa United El-Kanemi 1-0 Sunshine Stars Shooting Stars 2-0 Kwara United Wikki 1-0 Warri Wolves Dolphins 1-0 Rangers Nasarawa 2-1 Kano Pillars