UEFA na tuhumar Guardiola kan yin kamfen

Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bayern Munich ce ta doke Porto da ci 6-1 ranar Talata a Jamus

UEFA tana tuhumar kocin Bayern Munich Pep Guardiola bisa rigar da ya saka mai dauke da sakon yin kamfe ga dan jaridar Argentina wanda ya mutu a Brazil.

Kociyan ya saka rigar ne mai sakon neman a yi wa Jorge Lopez adalci wanda ya mutu a Brazil a lokacin da ake wasannin cin kofin duniya a shekarar 2014.

Hukumar kwallon kafar Turai na tuhumar Guardiola da shiga zarafin da bai shafi wasannin ba, kafin su kara da Porto a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata.

An kashe Jorge Lopez wanda aka fi sani da sunan Topo a Guarulhos dake Sao Paulo a watan Yulin 2014 a hatsarin mota lokacin da yake tsallaka titi.

Shi ma kocin Porto, Julen Lopetegui an tuhume shi da laifin nuna rashin da'a a fafatawar da suka yi a Jamus.