Hazard ne kashin bayan Chelsea — Zidane

Eden Hazard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea ce ke kan gaba a teburin Premier

Mataimakin kociyan Real Madrid Zinedine Zidane ya ce Eden Hazard ne kashin bayan Chelsea wanda ya sa suke haskaka wa a gasar Premier bana.

Hazarad dan kasar Belgium, mai shekaru 24, ya ci wa Chelsea kwallaye 18, sannan ya taimaka aka zura kwallaye sau 10 a kakar wasannin bana.

Rahotanni na cewa Madrid tana sha'awar ta dauko dan wasan, wanda ya tsawaita kwantiraginsa da Chelsea zuwa shekaru biyar a watan Fabrairun 2015.

Zidane ya danganta salon wasan Hazard dana Cristiano Ronaldo da kuma Lionel Messi na Barcelona.

Hazarad yana daga cikin 'yan wasan da aka fitar da za a zabo wanda ya fi yin fice a gasar Premier ta shekarar 2014-15 daga cikinsu.