Ya kamata a girmama Fabregas — Wenger

Cesc Fabregas Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Chelsea ta bai wa Arsenal tazarar maki 10 tsakani a teburin Premier

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce za a yi wa Cesc Fabregas tarbar girma a Emirates, idan sun zo yin wasa da Chelsea a gasar Premier ranar Lahadi.

Karawar da za su yi a ranar Lahadin ita ce wasa na biyu da Fabregas zai fuskanci kungiyar da ya yi wa wasa daga tsakanin 2003 zuwa 2011, tun lokacin da ya koma Chelse a watan Yunin bara.

Fabregas, mai shekaru 27 da haihuwa, ya buga wa Arsenal kwallo tun yana da shekaru 16, daga baya ya koma Barcelona a shekarar 2011.

Tun a baya Wenger ya ce baya yin nadamar kin sake dauko dan wasan tun lokacin da ya bar kulob din, illa dai ya yi bakin ciki a lokacin da ya bar Arsenal din.