Babu koci fiye da ni a Liverpool — Rodgers

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Liverpool za ta ziyar ci West Brom a gasar Premier wasan mako na 34 ranar Asabar

Brendan Rodgers ya ce babu wani koci sama da shi da ya kamata ya horar da Liverpool, kuma ya na fatan zai ci gaba da aiki a kungiyar a badi.

Liverpool tana mataki na biyar a kan teburin Premier, kuma Aston Villa ta fitar da ita daga gasar cin kofin FA a wasan daf da karshe da suka kara a makon jiya.

Rodgers, mai shekaru 42 da haihuwa shi ne kocin Liverpool na farko da bai dauki kofi ba a kakar wasa uku tun daga shekarar 1950.

Kocin ya maye gurbin Kenny Dalgish a shekarar 2012, ya kuma jagoranci kungiyar ta kammala gasar Premier a mataki na biyu a shekara ta biyu da ya kama aiki.

Ana rade radin cewar Jurgen Klopp wanda zai bar Borussia Dortmund a karshen kakar bana, zai maye gurbin Rodgers a kakar wasan badi.