Henderson ya tsawaita kwantiragi da Liverpool

Jordan Henderson Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana hasashen shi ne zai zama kyaftin din Liverpool idan Gerrard ya bar kungiyar a bana

Jordan Henderson ya sabunta kwantiraginsa da Liverpool zuwa tsawon shekaru biyar, kan kudi fan 100,000 a duk mako.

Henderson, mai shekaru 24 da haihuwa zai ci gaba da taka leda a Anfield har zuwa karshen kakar wasan 2020.

Dan kwallon dan kasar Ingila ya koma Liverpool ne daga Sunderland a shekarar 2011 kan kudi fam miliyan 20.

Mataimakin kyaftin din ya ci kwallaye biyar daga cikin wasanni 55 da ya buga wa Liverpool da tawagar kwallon kafar Ingila.

Haka kuma Liverpool din na shirin sabunta kwantiragin Daniel Sturridge da kuma na Philippe Coutinho kafin karshen kakar bana.