Kamfanin Nike ya kulla yarjejeniya da NFF

Amanju Pinnick Hakkin mallakar hoto nfftwitter
Image caption NFF ta sabunta kwantiraginta da koci Stephen Keshi

Kamfanin yin kayayyakin wasanni Nike, ya kulla kwantiragi da hukumar kwallon kafar Nigeria wato NFF, a inda tawagar kwallon kafar kasar za su yi amfani da kayayyakinsa.

A kunshin yarjejeniyar da suka kulla, kamfanin zai samar wa da tawagar kwallon kafar kasar ta maza da ta mata kayayyakin wasa daga 1 ga watan Afirilun 2015 zuwa shekarar 2018.

Tawagar kwallon kafar matasa 'yan kasa da shekaru 20 ne za su fara yin amfani da kayayyakin Nike din a gasar cin kofin matasa ta duniya da za a yi a New Zealand daga 31 ga watan Mayu.

Ranar Talatan nan ne da ta gabata hukumar kwallon kafar Nigeria ta sabunta kwantiraginta da koci Stephen Keshi zuwa tsawon shekaru biyu masu zuwa.