UEFA ta dauki mataki kan kofin Europa

Europa League draw Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Uefa za ta raba jaddawalin wasannin daf da karshe ne a kofin Europa ranar Juma a

Hukumar kwallon kafar Turai UEFA za ta yi kokarin kauce wa hada wasa tsakanin kungiyoyin Rasha da kuma na Ukraine a wasan daf da karshe a gasar cin kofin Europa.

Hukumar za ta yi haka ne domin kada kungiyoyin su fada yankin da ake rikici a kudancin Ukraine.

UEFA za ta raba jaddawalin wasannin daf da karshe a kofin Europa ranar Juma a da ake hangen Dnipro Dnipropetrovsk da Dynamo Kiev dukkanninsu daga Ukraine da kuma Zenit St Petersburg daga Rasha za su iya samun tikitin wasannin.

Idan dukkansu suka kai wasan daf da karshe, hukumar za ta hada wasa ne tsakanin Dnipro da Dynamo, sannan Zenith ta kara da wacce ta samu gurbi na hudu.

Haka kuma hukumar ta sanar da cewar za a buga wasan karshe idan kungiya daga Rasha da kuma ta Ukraine suka rage a gasar a Poland ranar 27 ga watan Mayu.

Ranar Alhamis ne za a tantance kungiyoyin da za su kai wasan daf da karshen idan suka buga wasanninsu na biyu.