China za ta gina filin wasa a Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tawagar Ivory Coast ce ta lashe gasar kofin Afrika a 2015

China za ta gina katafaren filin wasa mai cin 'yan kallo 60,000 a kasar Ivory Coast kafin lokacin gasar cin kofin kwallon Afrika a 2021.

Za a gina filin wasan a birnin Abidjan, inda za a soma ginin a watan Janairun 2016 kuma za a shafe shekaru biyu kafin kamalla shi.

Kakakin ma'aikatar wasanni a Ivory Coast ya ce "kyauta ce daga China".

A yanzu haka akwai wani babban filin wasa a Abidjan mai cin 'yan kallo 35,000 mai suna Houphouet-Boigny wanda aka gina a shekarar 1960.