UEFA: Barcelona za ta hadu da Bayern Munich

Hakkin mallakar hoto Getty

Barcelona za ta hadu da Bayern Munich a wasan zagayen kusa da karshe a gasar zakarun Turai wanda tsohon kocin tawagarta Pep Guardiola ke jagoranta.

Haka kuma Juventus za ta kara da Real Madrid a daya wasan zagayen kusa da karshen.

Za a buga wasan farko ne a ranar 5 da 6 ga watan Mayu sai kuma wasa na biyu baya mako guda.

Kocin Bayern, Guardiola ya lashe kofuna 13 a matsayinsa na manaja, ciki har da gasar zakarun Turai a 2009 da kuma 2011 a lokacin yana Barcelona.

Kocin Real, Carlo Ancelotti zai hadu da tsohuwar tawagarsa watau Juventus wacce ya jagoranta daga shekarar 1999 zuwa 2001.