Giggs ne zai gaje ni a United — Van Gaal

Van Gaal Giggs
Image caption Giggs ne ya jagoranci United wasanni hudu a lokacin da aka kori David Moyes daga aiki

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce yana da tabbacin Ryan Giggs ne zai gaje shi idan ya bar kungiyar.

Giggs, mai shekaru 41 da haihuwa, shi ne ya jagoranci United wasanni hudu, bayan da aka kori David Moyes daga aikin.

Tsohon dan wasan United wanda ya buga mata wasanni 963 ya lashe wasanni biyu da canjaras daya aka doke shi wasa guda lokacin da ya horar da United din.

Van Gaal, mai shekaru 63, zai cika shekara guda da United a karshen kakar bana, kuma sai a shekarar 2017 kwantiraginsa da United zai kare.

Kociyan ya ce yana bai wa Giggs wasu ayyukan, a inda kuma yake gudanar da su kamar yadda ya kamata.