"Toure yana jin dadin zama a Man City"

Yaya Toure Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Toure ya koma City ne daga Barcelona a shekarar 2010

Kociyan Manchester City Manuel Pellegrini ya ce Yaya Toure yana jin dadi buga tamaula da kulob din da ke Ettihad.

Rahotanni na cewa dan kwallon dan kasar Ivory Coast ya ce yana neman kungiyar da zai fuskanci kalubale mai yawa.

Saura shekaru biyu kwantiragin Toure mai shekaru 31, ya kare da Manchester City, wanda ake cewa kila ya koma Paris St-Germain a badi.

Mai kula da harkokin buga kwallon Toure, Dimitry Seluk zai tattauna da City, bayan da ya ce manyan kungiyoyin Turai na zawarcin dan wasan.

Toure ya koma City ne daga Barcelona kan kudi fam miliyon 24 a shekarar 2010, kuma ya taka rawar gani a lokacin da kungiyar ta dauki kofin Premier a shekarar 2012 da kuma 2014.