Zaben gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta BBC ta bana

An bayyana sunayen 'yan wasa biyar mata da za a fitar da daya daga cikinsu a wacce BBC za ta karrama da lambar gwarzuwar 'yar kwallon kafar ta bana.

Wannan dai shi ne karon farko da BBC za ta fara karrama 'yar kwallon kafar da ta fi yin fice a wasa.

'Yan wasa biyar da aka bayyana sun hada da Veronica Boquete ta Spaniya da Nadine Kessler ta Jamus da Kim Little ta Scotland da Marta ta Brazil da kuma Asisat Oshoala ta Nigeria.

Masu sha'awar kwallon kafa na da damar kada kuri'unsu ga wanda suke so tun daga yanzu har zuwa ranar 11 ga watan Mayun nan.

Kwarrarru ne suka fitar da 'yan wasa biyar da suka fi yin fice a bana da suka hada mahukunta da 'yan jaridu da masu horar wa da tsoffin 'yan wasa da suka yi fice.

Masu sha'awar yin zaben za su iya kada kuri'arsu ta shafin BBC ko ta aika sako ga lamaba +44 7786 20 20 04.

Za a iya tura sako da lambar 'yar wasan da aka zaba. Aika 1 don zaben Veronica Boquete, 2 don zaben Nadine Kessler, 3 don zaben Kim Little, 4 don zaben Marta da kuma 5 don zaben Asisat Oshoala.

Latsa nan domin kada kuri'a

Veronica Boquete (Spain and Frankfurt)

Hakkin mallakar hoto Getty

Kyaftin din tawagar kwallon kafar matan Spaniya mai shekaru 27 da haihuwa, ita ce ta jagoranci kasar da suka samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya a karon farko.

Kwararriyar 'yar wasa ce wacce ta lakanci zura kwallo a raga, kuma ita ce kashin bayan Spain a inda ta ci kwallaye 29 daga wasanni 42 da ta buga.

Ta kuma yi suna a fafutar da ta yi a shekarar 2013, a inda ta bukaci hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta saka 'yan kwallon kafa mata a cikin jerin wasannin kwamfutar hukumar, ta kuma samu mutane 20,000 da suka rattaba hannu a goyon bayanta.

Ta ce "Na yi matukar murna da aka saka ni cikin jerin wadanda za fitar a kyautar 'yar wasan da ta fi yin fice da BBC za ta karrama a bana. Hakan na nufin na taka rawar gani ke nan gabaki dayan shekarar."

Nadine Kessler (Germany and Wolfsburg)

Hakkin mallakar hoto Getty

Ita ce kyaftin din daya daga cikin fitatciyar kungiyar kwallon kafar mata a Turai, kuma kashin bayan tawagar kwallon kafar matan Jamus, babu wata kyauta da Kessler ba ta lashe ba a fagen taka ledar mata a karo da dama.

Mai shekaru 27 da haihuwa, kyaftin din Wolfsburg ta Jamus ta lashe kofin zakarun Turai karo biyu da kuma kofin Frauen na Jamus a bara.

Wadan nan nasarori ne ya sa aka zabe ta a 'yar wasan da ta fi yin fice a duniya da FIFA ta karramata a shekarar 2015, a inda ta maye gurbin Nadine Angerer ta Jamus.

Sai dai kuma tana fama da jinyar rauni akai-akai da ake hasashen zai hanata haskaka wa a gasar cin kofin duniya da Canada za ta karbi bakunci a bana.

Ta ce "Kyauta ce mai mahimmaci... gare mu 'yan wasa da irin goyon bayan da muke samu daga masu kyaunarmu, shi ne mafi fifico. A jamus muna kiran kyautar da mutun na 12 a filin wasa".

Kim Little (Scotland and Seattle Reign)

Hakkin mallakar hoto Getty

Little yar kwallon Scotland ta yi fice a gasar kwallon kafar Amurka a shekarar nan, a inda take buga gurbin 'yar wasan tsakiya mai cin kwallo.

'Yar wasan ta ci kwallaye 16 a raga, a inda aka zabe ta a matsayin 'yar wasan da ta fin fice a watanni uku a jere, aka kuma zabe ta a wadda ta fi taka rawar gani a gasar Amurka a bara, a inda kungiyarta ta kai wasan karshe kuma Kansas ta doke su a karawar.

Duk da cewar shekarunta 24 da haihuwa, ta zama kwararriyar 'yar wasan kwallon kafa tun a shekarar 2006, ta kuma lashe kyautar 'yar wasan da ta fi yin abin- a-zo-a-gani a shekarar 2013, wacce kungiyar kwararun 'yan wasa suka karrama ta.

Ta ce "Duk da gogayya da tarin taurarin 'yan wasan da suke fadin duniya da kuma na gasar kwallon kafar Amurka wato NWSL, ace an hangi gudunmawar da kake bayar wa hakika abin farinciki ne."

Marta (Brazil and FC Rosengard)

Hakkin mallakar hoto Getty

Marta babu tantama sunane da ya shahara a wasan kwallon kafar mata ta duniya.

Mai shekaru 29 da haihuwa, yar kwallon Brazil wacce take cin kwallo daya a kalla a duk wasan da ta buga wa kasarta a manyan wasanni 91, har yanzu tana kan ganiyarta.

Ta kuma lashe gasar kasar Sweden a bara kuma karo na shida, koda yake ta rasa kofin zakarun Turai a inda aka doke su a wasan karshe, amma ta dauki kofin kalubalen Sweden a bara.

Ta ce "na yi murna da aka saka sunana a cikin 'yan takara, a yanzu ma ji nake yi na lashe kayutar tun da ina cikin 'yan takara biyar da aka fitar. Abu ne mai mahimmaci saboda al'umma ne suke yanke hukunci wadan da suke bibiyar wasanninka."

Asisat Oshoala (Nigeria and Liverpool)

Hakkin mallakar hoto Getty

Tana da karsashi da nuna kwazo duk da cewar shekarunta 20 da haihuwa, Asisat Oshoala ita ce 'yar wasan Afirka ta farko da ta fara buga gasar kwallon kafar Ingila wato Women's Super League.

Ta kuma lashe kyautar 'yar kwallon kafar Afirka da ta fi yin fice da kuma kyautar matashiyar da ta fi yin kwazo a shekarar 2014, sannan ta koma buga gasar Women's Super League ta Ingila a bana daga kulob din Rivers Angels.

Wacce ake yi wa lakani da suna "Seedorf" sunan fitatcen dan kwallon nan Clarence. Kuma ita ce wacce ta fi yin fice a gasar matasa 'yan kasa da shekaru 20 ta duniya da aka kammala a bana a Canada, a inda ta taimaka wa Nigeria lashe kofin bana, kuma shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya ba ta lambar girmama wa.

Ta ce "Na ji dadi matuka. Na saka kaimi a bara matuka, amma na yi mamaki da aka zabe ni cikin 'yan takara. Wannan kyautar tana da mahimmaci ga wasannin kwallon kafar mata - zai kara mana kwarin gwiwa ta yadda sauran kasashe za su dunga marawa wasannin mata fiye da yadda ake yi wa 'yan kwallon kafa maza."