Darajar Hazard ta kai fam miliyan 200 — Mourinho

Hazard Mourinho Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chelsea tana matakinta na daya a kan teburin Premier

Jose Mourinho ya ce kowace kafar Eden Hazard daya ta kai darajar kudi fam miliyon 100, idan Real Madrid tana son daukarsa daga Chelsea.

Hazard, mai shekaru 24 da haihuwa, ya bai wa Chelsea gudunmawa a gasar wasan bana a inda ya ci kwallaye 18 a gasar.

Mourinho ya ce "Idan har Madrid tana son ta dauki Hazard, sai ta biya Chelsea fam miliyan 100 da kuma bata fitatcen dan wasa daya ko kuma yan kwallonta uku".

Kocin ya kara da cewar Hazard kwararren dan wasa ne, sannan tauraruwarsa tana haskawa, kuma yana da karancin shekaru.

Mourinho ya ce yana da kyakkawar alaka da Madrid saboda haka idan suna zawarcin dan wasan zai sani ba wai ya ji ta bayan gida ba.