'Yan wasan Chelsea 6 a cikin fitattun Premier 11

PFA Team of the Year
Image caption Ranar Lahadi ne za a karrama wadan da suka taka rawar gani a gasar Premier bana

'Yan wasan Chelsea shida sun hada da Branislav Ivanovic da John Terry da Gary Cahill da Nemanja Matic da Eden Hazard da kuma Diego Costa.

Sauran 'yan kwallon da aka zabo sun hada da Ryan Bertrand na Southampton da Harry Kane na Tottenham.

David De Gea ne mai tsaron raga, sai kuma dan wasan Liverpool Philippe Coutinho da kuma Alexis Sanchez na Arsenal da suke cikin wadan da aka zaba.

Za a sanar da sunan wanda ya lashe kyautar dan wasan Premier da kuma matashin dan kwallon da ya fi kwazo a bana ranar Lahadi a Grosvenor House da ke Landon.