Torino ta doke Juventus a wasan hamayya

Torino Juventus Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Juventus na daf da daukar kofin Seria A na 31 jumulla

A karon farko kungiyar Torino ta doke Juventus da ci 2-1 a wasan hamayya a gasar Seria A wasannin mako na 32 da suka buga ranar Lahadi.

Juventus ce ta fara cin kwallo ta hannun Pirlo, sai dai kuma daf da za a tafi hutun rabin lokaci Darmian ya farke kwallo sannan Quagliarella ya kara ta biyu a raga.

Rabon da Torino ta doke Juventus tun shekaru 20 da suka wuce, a in da ta samu nasara da ci 2-1 a gidan Juventus a gasar ta kasar Italiya.

Torinon ta kuma taka wa Juventus burkin yawan lashe wasanni 17 a jere da kuma karya tarihin cinye wasannin hamayya bakwai da ta yi.

Juventus tana mataki na daya a teburin Serie A da maki 73, a inda take harin daukar kofi na hudu a jere kuma na 31 jumulla.

Ga sakamakon wasu wasannin da aka buga:

  • Atalanta 2 - 2 Empoli
  • Genoa 3 - 1 Cesena
  • Lazio 1 - 1 Chievo
  • Parma 1 - 0 Palermo
  • Verona 3 - 2 Sassuolo