Hazard zai yi fice a duniyar tamaula - Shearer

Eden Hazard Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Chelsea za ta kara da Leicester City ranar Laraba a gasar Premier

Alan Shearer ya ce dan kwallon Chelsea Eden Hazard zai iya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta duniya wato Ballon d'Or.

Hazard shi ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi yin fice a gasar Premier a inda aka karrama shi ranar Lahadi a Landan.

Shearer ya ce lashe kyautar da dan kwallon ya yi da kuma kofin Premier da zai dauka da Chelsea zai kara masa kwarin gwiwa a wasanninsa.

Hazard ne ya karbi lambar yabo ta matashin da ya fi haskakawa a gasar Premier a shekarar 1995.

Chelsea tana mataki na daya a teburin Premier da maki 77, a inda ta bai wa Manchester City da Arsenal tazarar maki 10 tsakani, kuma tana da kwanta wasa da za ta yi da Leicester City.