Bale zai buga karawa da Juventus

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga, za kuma ta yi wasa da Almeria ranar Laraba

Gareth Bale zai buga wasan daf da karshe a gasar cin kofin zakarun Turai da Real Madrid za ta kara da Juventus.

Dan wasan, mai shekaru 25 da haihuwa, ya yi jinyar kwanaki 10, amma ana sa ran zai fara yin atisaye da 'yan wasa a makonnan.

Madrid wacce za ta buga gasar La Liga da Almeria ranar Laraba, tana kuma sa ran Karim Benzema shi ma zai buga wasan a Italiya.

Benzema ya ji rauni ne a wasan farko da suka fafata da Atletico a wasan daf da na kusa da karshe a gasar kofin zakarun Turan.

Idan 'yan wasan biyu suka dawo taka leda, zai kara wa Madrid kwarin gwiwa a kokarin da take yi na lashe kofin Turai karo na 11 da kofin La Liga.