Za a bai wa kulob din da ya samu gurbin Premier £120m

EPL logo Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption masana tattalin arzikin tamaule ne suka fitar da wannan bayanin

Masana tattalin arzikin tamaula sun ce kulob din da ya samu gurbin shiga gasar Premier zai karbi kudi da zai kai fam miliyan 120.

Hakan na nufin kudaden da kulob din Watford da Bournemouth da suka samu tikitin shiga gasar Premier daga gasar Championship za su karba kowannen su.

Wartford ta samu gurbin shiga gasar Premier badi ne a ranar Asabar, a inda Bournmouth ta samu nata tikitin a ranar Litinin.

Wani masani kan kasuwanci Trevor Birth ya ce samun tikitin buga gasar Premier wani al'amari ne mai mahimmanci.

Ya ce "kusan kasashe 200 ke nuna gasar, wanda ya kai yawan mutane biliyan hudu ne ke kallon wasannin Premier".

Wannan shi ne karon farko da Bournmouth za ta shiga gasar Premier, yayin da Wartford ta koma gasar bayan shekaru takwas da ta bar gasar.

Rob Wilson na jami'ar Sheffield Hallam ya shaida wa BBC cewa kungiyoyin za su karbi fam miliyan dari daga kudaden nuna wasanninsu a talabijin da kuma karin fam miliyan 20 daga kudin tallace - tallace.