Chelsea ta ci Leicester City kwallaye 3-1

Chelsea FC
Image caption Saura wasa daya za ta lashe ta dauki kofin Premier bana

Chelsea ta hada maki uku, bayan da ta doke Leicester City da ci 3-1 a kwantan wasan Premier da suka buga a filin wasa na King Power.

Leicester ce ta fara cin kwallo ta hannun Albrighton daf da za a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dowo wasan ne da minti uku Drogba ya farke kwallon, kuma Terry ya kara ta biyu kafin Ramires ya ci ta uku a raga.

Har yanzu Chelsea tana matakinta na daya a teburin Premier ta kuma bai wa Manchester City da Arsenal tazarar maki 13 tsakani.

Chelsea za ta karbi bakuncin Crystal Palace a wasan mako na 35 ranar Lahadi a Stamford Bridge.