An daure Facey kan cinikin wasan tamaula

Delroy Facey Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Delroy Facey tsohon dan wasan Bolton da West Brom da kuma Hull City

An daure tsohon dan kwallon Premier Delroy Facey shekaru biyu da rabi, bayan da kotu ta same shi da laifin cinikin wasan kwallon kafa.

Kotun Birmingham ce ta samu Facey da laifin hada baki da bai wa 'yan wasa cin hanci domin a cefanar da wasan kwallon kafa.

Alkali Mary Stacey ta ce "Laifin da Facey ya aikata kamar wanda ya harbi zuciyar kwallon kafa ce da kibiya".

Sai dai kuma Facey wanda ya buga wa Bolton Wanderers da West Bromwich Albion da kuma Hull City ya karyata cewar ya aikata ba dai-dai ba.