Mayweather ya kalubalanci Pacquiao

Floyd Mayweather
Image caption 'Yan wasan biyu za su fafata ne a Las Vegas ranar Asabar

Floyd Mayweather ya kalubalanci Manny Pacquiao wanda za su dambata ranar Asabar, inda ya ce ya kamata ya dinga samun kudade da yawa a dambe.

Damben da za su yi shi ne wanda zai fi tsada a duniya a inda 'yan damben za su raba kudi da zai kai £150m a tsakaninsu, duk da ba a gama tantance yawan kudin da za su samu ba.

Bayan sun kammala damben a ranar Asabar Mayweather zai karbi kashi 60 cikin dari, sannan a bai wa Pacquiao sauran kashi 40 na kudin kallon da za a samu a karawar.

Sai dai Mayweather dan Amurka ya ce Pacquiao dan kasar Philiphines baya kula da kansa kamar yadda ya kamata.

Ya kara da cewa da a ce zai yi aiki tare da shi zai iya samun kudi da zai kai $100m.

Ya kuma ce hakika ba a kyauta masa ba wajen rabon kudin damben, amma karawar domin a samu arziki za su yi.