Real Madrid ta doke Almeria da ci 3-0

Real Madrid Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Madrid tana nan a matsayinta na biyu a teburin La Liga

Real Madrid ta doke UD Almeria da ci 3-0 a gasar La Ligar Spaniya wasan mako na 34 da suka buga a Santiago Bernabeu ranar Laraba.

Madrid ta zura kwallayen ne ta hannun Rodríguez sai Dos Santos da ya ci kansu, kafin Arbeloa ya kara ta uku saura minti shida a tashi daga wasan.

Da wannan nasarar Madrid tana matakinta na biyu a teburin La Liga da maki 82, kuma saura wasanni hudu ya rage a kammala gasar bana.

Real Madrid za ta ziyarci Sevilla a wasan mako na 35 a ranar Asabar.