Arsenal ta hana babar Ainsley halartar wasanninta

Ainsley Maitland-Niles Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana sa ran dan wasan zai yi fice a fagen tamaula a duniya

Kungiyar Arsenal ta dakatar da mahaifiyar dan wasanta Ainsley Maitland-Niles daga halartar wasannin da take yi, bayan da ta tayar da hatsaniya.

Matar ta tayar da hatsaniya tsakaninta da babban jami'in Arsenal Dick Law da eja din danta, har ma ta yi ikirarin za ta fitar da shi daga wasan da yake buga wa a lokacin.

Daga karshe Arsenal ta kira jami'an tsaro, a inda suka yi gaba da Jule Niles, sai dai ba'a tuhumeta ba, illa dai an ja mata kunne ta guji tayar da hayaniya.

Maitland-Niles, mai shekaru 17, ya fara buga tamaula da Arsenal tun yana da shekaru tara, kuma ya buga wa babbar kungiyar wasa a bana.

Sai dai kuma Arsenal tana fargabar Jule Niles za ta iya hana matashin dan wasan wanda yake zaune da mahaifiyarsa halartar wasannin Arsenal.