Martens ya rasu bayan da ya fadi a filin wasa

Gregory Mertens
Image caption Dan kwallon Lokeren ya fi kowanne dan wasa kuzari a kulob din

Dan kwallon Belgium Gregory Mertens ya rasu bayan da zuciyarsa ta tsaya da aiki kwanaki uku da ya fadi a lokacin da suke yin wasa.

Dan wasan, mai shekaru 24, wanda yake buga wa Lokeren tamaula ya fadi ne a filin wasa a ranar Litinin lokacin da suka kara da karamar kungiyar Genk.

Tun a lokacin likitoci suka duba lafiyarsa a cikin filin suka kuma saka shi a cikin naurar da take taimakawa mutun yin numfashi.

Gregory ya mutu da karfe 04:30 na yammacin ranar Litinin.

Martens ya ci gwajin da likitocin kulob din Lokeren suka yi masa kamar yadda hukumar kwallon kafar Turai ta bukata, kuma shi ne dan wasan da ya fi kuzari a kulob din.

Dan kwallon ya je Lokeren a Janairun 2014 daga Cercle Brugge, a inda ya buga wasanni 15 a kakar wasan bana.