Carver ya gayyaci magoya bayan Newcastle biyu

John Carver Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption John Carver yana shan matsi daga wajen magoya bayan Newcastle United

Kociyan Newcastle John Carver ya gayyaci wasu magoya bayan kulob din su biyu wadan da suka kalubalance shi a wasan da Swansea ta doke su tattaunawa.

Carver, mai shekaru 50, ya sha kalubale daga magoya baya a lokacin da Swansea ta doke su da ci 3-2 a gasar Premier a St James' Park.

Rashin nasarar da suka yi shi ne na bakwai da aka doke su a wasanni a jere, kuma saura maki biyar su shiga sawun kungiyoyin da za su iya barin gasar Premier bana.

Carver ya ce ya gayyaci magoya bayan ne, domin su fuskanci juna ya kuma fayyace musu irin kokarin da yake yi kan kungiyar ta ci gaba da zama a gasar Premier.

Kociyan ya kuma ce zai yi farin cikin sauraren abubuwan da za su shaida masa da kuma shawarwarin da za su bashi.