Kaka na fatan Brazil za ta gayyace shi

Kaka Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kaka yanzu yana murza leda ne a Amurka

Tsohon gwarzon dan kwallon kafa na duniya Kaka ya ce har yanzu yana da rawar da zai taka a tawagar kwallon kafar Brazil idan aka gayyace shi.

Brazil tana shirye-shiryen tunkarar gasar Copa America da za a fara a cikin watan Yuni mai zuwa.

Kaka, mai shekaru 33, wanda ke taka leda a gasar Amurka da kulob din Orlando City yana daga cikin 'yan wasan da suka buga wa Brazil kofin duniya da ta karbi bakunci a shekarar 2014.

Bayan kammala gasar ne aka sallami koci Luiz Felipe Scolari aka maye gurbinsa da Dunga wanda zuwa yanzu ya lashe wasanni sada zumunta takwas da suka yi.

Kaka tsohon dan kwallon AC Milan da Real Madrid ya ce bai wa Dunga ragamar horar da Brazil ya dawo da martabar kasar a fagen kwallon kafa a duniya.