Robben zai yi jinyar makonni biyar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Robben zai shafe lokacin yana jinya

Arjen Robben ba zai kara buga wasa ba a kakar wasa ta bana tare da Bayern Munich.

Hakan ya biyo bayan raunin da ya ji a kafarsa abin da ya sa zai yi jinyar makonni biyar.

Robben ya ji rauni ne a wasansu da Borussia Dortmund na gasar cin kofin Jamus a ranar Talata.

Shi ma dan kwallon Bayern, Robert Lewandowski ya ji rauni bayan karya kashin hancinsa.

Amma dai ana saran Lewandowski zai buga wasansu da Barcelona a gasar zakarun Turai a ranar 6 ga watan Mayu.

A cikin makon da ya wuce ne Bayern Munich ta lashe kofin gasar Bundesliga a karo na 25.