Suarez ya ci wa Barca kwallaye uku

Luis Suarez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Saura wasanni uku kenan a kammala gasar bana

Barcelona ta zazzaga wa Cordoba kwallaye 8-0 a gasar La Liga wasan mako na 35 da suka yi ranar Asabar.

Louis Suarez ya ci kwallaye uku a wasan, kuma karon farko da ya yi hakan tun lokacin da ya koma Barcelona daga Liverpool kan kudi fam miliyan 75.

Shi kuwa Messi kwallaye biyu ya zura a raga, kuma jumulla ya ci 51 a kakar wasan bana, sai Ivan Rakitic da Gerard Pique da kuma Neymar da kowannen su ya ci kwallo guda-guda.

Da wannan nasarar da Barcelona ta samu ya sa ta tsawaita yawan lashe wasanni 15 a dukkan karawar da ta yi, kuma ba a ci ta a fafatawa 16 ba.

Sauran wasanni uku a kammala gasar bana, kuma Barcelona tana matakinta na daya da maki 87, kuma za ta kara da Real Sociedad da Atletico Madrid da kuma Deportivo la Coruna.