Bournemouth ta lashe kofin Championship

Bournemouth  FC Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bournemouth sai da tattalin arzikin kulob din ya kusa karye wa a shekarar 2008

Kungiyar Bournemuth ta lashe gasar Championship ta bana, bayan da ta doke Chalton da ci 3-0 ranar Asabar a wasan karshe na gasar.

Bournemouth din ta ci kwallayen ne ta hannun Matt Ritchie Ritchie wanda ya zura guda biyu a raga, kuma Harry Arter ya ci daya a minti na 12 da fara wasan.

Wannan nasarar da Bournemouth ta samu dai ta ba ta cancantar buga gasar Premier ta badi, kuma za ta karbi kudi da zai kai fam miliyan 12 domin nuna wasanninta a talabijin a gasar badin.

Bayan kammala gasar Championship ta bana a inda kowacce kungiya ta buga wasanni 46, Bournmouth na da maki 90, Watford ta kammala da maki 89 ta kuma samu gurbin Premier badi.

Sauran kungiya daya ake nema da za ta cike gurbi na uku, a inda za a fafata tsakanin Norwich da Middlesbrough da Brentford da kuma Ipswich domin fitar da wadda za ta buga Premier badin.