Mayweather ya doke Pacquiao

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mayweather ke nan ya naushi Pacquiao da hannun dama a karawar tasu a MGM Grand Garden Arena

Dan damben boksin na Amurka Floyd Mayweather ya yi nasara a kan abokin karawarsa Manny Pacquiao dan Philippines da yawan maki.

Alkalan damben uku sun bayar da maki kamar haka; 118-110 da 116-112 da kuma 116-112, a karon-battar da suka yi a Las Vegas da misalin karfe biyar na Asubar Lahadin nan.

Yanzu Mayweather mai shekara 38 ya kara kambun WBO na matsakaita nauyi a kan na WBC da WBA da daman yake rike dasu.

Da wannan nasara yanzu, ba a taba buge shi a wasanninsa 48,a shekaru 19 ba, kuma ya zama dan damben da ya fi fice na zamaninsa.

Shi kuwa Manny Pacquiao wannan shi ne karo na shida da ya yi rashin nasara a dambensa.

An yi kiyasin damben wanda aka yi wa lakabi da damben karni ya samar da dala miliyan 400, inda 'yan damben biyu za su raba kusan dala miliyan 230, amma Mayweather zai samu kaso mafi yawa.

Bayan karon-battar Mayweather ya ce, ba zai sake dambe ba a watan Satumba kafin ya yi ritaya.

Sai dai ana ganin burin kawar da tarihin bajintar Rocky Marciano ta dambe 49 ba tare da an doke shi ba, ya sa ya ci gaba da damben.

Amir Khan da Kell Brook 'yan Birtaniya su ne na gaba a jerin wadanda ake sa ran za su gwabza da Mayweather.