Chelsea ta lashe kofin Premier karo na hudu

Eden Hazard
Image caption Chelsea ta dauki kofin Premier na hudu a cikin shekaru 11

Kungiyar Chelsea ta dauki kofin Premier bana kuma karo na hudu, bayan da ta doke Crystal Palace da ci daya mai ban haushi a Stamford Bridge ranar Lahadi.

Chelsea ta ci kwallo ne ta hannun Eden Hazard a bugun fenariti daf da za a tafi hutu, bayan da James McArthur ya yi masa keta a da'ira ta 18.

Chelsea ta dauki kofin bana kuma na hudu a cikin shekaru 11 duk da sauran wasanni uku ya rage a kammala gasar.

Kungiyar ta buga wasanni 35 ta lashe guda 25 ta buga canjaras a wasanni takwas aka doke ta wasanni biyu ta kuma hada maki 83.

Chelsea za ta buga sauran wasanni uku da suka rage da Liverpool a Stamford Bridge sannan ta ziyarci West Brom daga karshe ta kara da Sunderland a gida.