"Wilshere na bukatar yin jinyar shekara daya"

Jack Wilshere Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wenger ya ce Wilshere yana bukatar lokaci mai tsawo kafin ya dawo kan ganiyarsa

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce Jack Wilshere yana bukatar yin jinyar shekara daya ko kuma biyu kafin ya dawo kan ganiyarsa.

Dan wasan, dan kasar Ingila, yana fama da rauni ne a agara, inda kocin ya ce ya kamata ya yi jinya mai tsawo kafin ya dawo murza leda.

Rabon da Wilshere ya buga wa Arsenal tamaula ya kai watanni biyar, amma ya zauna a kan benci a fafatawar da suka yi da Chelsea.

Wilshere ya ji raunin ne bayan da Paddy McNair ya yi masa keta a wasan da suka yi da Manchester United a watan Nuwamba.