Gasar Premier Nigeria wasannin mako na 7

Nigerian League Hakkin mallakar hoto glonpfl Twitter
Image caption An shiga wasannin mako na bakwai a gasar Premier Nigeria

Za a ci gaba da buga gasar Premier Nigeria wasannin mako na bakwai tsakanin El-Kanemi Warriors da Akwa United ranar Lahadi.

Sauran wasannin da za a kara Giwa FC za ta karbi bakuncin Bayelsa United, Sunshine Stars kuwa ta ziyarci Heartland da kuma wasa tsakanin Wikki Tourist da Rangers.

Gabros za ta karbi bakuncin Enyimba ta garin Aba, yayin da Dolphins za ta barje gumi tsakaninta da Lobi Stars sai Sharks ta karbi bakuncin Taraba FC.

Ga jerin wasannin da za a buga ranar Lahadi:

  • Sharks vs FC Taraba
  • Dolphins vs Lobi Stars
  • Gabros FC vs Enyimba
  • Giwa FC vs Bayelsa Utd
  • El-Kanemi vs Akwa Utd
  • Wikki vs Rangers
  • Heartland vs Sunshine Stars
  • Nasarawa Utd vs Abia Warriors
  • Kwara Utd vs Kano Pillars