Roma ta samu gurbin shiga kofin zakarun Turai

Seydou Doumbia
Image caption Saura wasanni hudu a kammala gasar Serie A ta Italiya

Roma ta samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai na badi, bayan da ta doke Genoa da ci 2-0 a filin wasa na Olimpico ranar Lahadi.

Seydou Doumbia da kuma Alessandro Florenzi ne suka ci wa Roma kwallayen biyu a raga, wanda ya ba ta damar kai wa mataki na biyu a teburin Serie A ta Italiya.

Lazio ta yi kasa zuwa matsayi na uku, bayan da ta tashi kunnen doki da Atalanata, a inda Roma ta ba ta tazarar maki daya tsakani.

Ita kuwa Fiorentina ta koma matsayi na biyar a gasar da maki 52, ta bai wa Genoa tazarar maki biyu wacce ke mataki na bakwai.

Inter Milan ta tashi wasa ne da Chievo babu ci, yayin da Udinese ta doke Hellas Verona da ci daya mai ban haushi a ranar Lahadin.