Manchester City ta doke Tottenham da ci 1-0

Sergio Aguero
Image caption Aguero ya ci kwallaye 22 a gasar Premier bana

Manchester City ta samu nasara a kan Tottenham da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 35 da suka yi a White Hart Lane.

City ta ci kwallo ne ta hannun Sergio Aguero a minti na 29 da fara wasan kuma kwallo ta 22 da ya ci a gasar Premier bana.

Manchester City ta ci gaba da rike matakinta na biyu a teburin Premier da maki 70, za kuma ta kara a gasar mako na 36 da QPR a Ettihad ranar Lahadi

Tottenham kuwa tana nan a matsayinta na shida a teburin da maki 58, sannan kuma za ta ziyarci Stoke City a ranar Asabar.