Carver zai ci gaba da horar da Newcastle

John Carver Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dukkan jami'an Newcastle sun amince su hada hannu su tserar da kulob din daga barin Premier bana

Kociyan Newcastle United John Carver zai ci gaba da horar da kulob din zuwa karshen kakar bana, a kokarin da suke yi na kauce wa barin gasar.

Carver, mai shekaru 50, ya zargi mai tsaron baya Mike Williamson da yin keta da gangan da aka kore shi daga wasan da suka yi da Leicester ranar Asabar.

Haka kuma mujallar Daily Telegraph ta ruwaito cewar kyaftin Fabricio Coloccini da kuma Tim Krul sun yi cacar baki da kocin bayan da aka tashi daga karawar.

Kulob din ya bayar da sanarwar cewa "John ne zai ci gaba da jan ragamar Newcastle don karasa wasanni ukun da suka rage".

Newcastle zai karbi bakuncin West Brom ranar Asabar, kuma yana mataki na 15 a teburin Premier, maki biyu ya rage ya shiga jerin kungiyoyin da za su iya barin gasar bana.