Za mu dauki fansa a kan Munich — Messi

Munich Bayern Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Munich ce ta fitar da Barca da ci 7-0 a gasar kakar wasan 2012/13

Lionel Messi ya ce za su dauki fansa a kan Bayern Munich idan suka hadu ranar Laraba a gasar cin kofin zakarun Turai wasan daf da karshe.

Munich ce ta fitar da Barcelona a wasan daf da karshe a gasar kakar 2012/13, aka kuma ci Barcelona jumullar kwallaye 7-0 a wasan gida da waje.

Messi ya ce "Fitar da su da aka yi a lokacin ya ba ta musu rai matuka amma yanzu ya wuce, za mu fuskance su da sabon salon wasa haka suma za su tunkare mu".

Doke Barca 7-0 a haduwar da suka yi da Munich shi ne wasan da aka fi zazzaga wa Barca kwallaye a raga a gasar cin kofin zakarun Turai a tarihi.

Kocin Bayern Per Guardiola ya horar da Barca shekaru hudu, a inda ya dauki kofin La Liga guda uku da kofin zakarun Turai kafin ya koma Munich a shekarar 2013.