Barcelona ta zura kwallaye uku a ragar Munich

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Messi ya ci kwallaye 77 a tarihin gasar zakarun Turai

Barcelona ta doke Bayern Munich da ci 3-0 a gasar cin kofin zakarun Turai wasan daf da karshe karon farko da suka yi a Camp Nou.

Messi ne ya ci kwallaye biyu a wasan, a inda Neymar ya kara ta uku daf da za a tashi daga karawar.

A dai-dai irin wannan lokacin a shekarar 2012/13 Munich ce ta fitar da Barca da ci 7-0 jumulla a fafatawar da suka yi gida da waje a gasar.

Bayern Munich za ta karbi bakunci Barcelona a wasa na biyu a gasar ranar Talata 12 ga watan Mayu.