Real Madrid ce ta fi arziki a duniya

Real Madrid Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gasar kasar Spaniya za ta samu tsaiko sakamakon takaddama da ake yi tsakanin gwamnati da FA

Real Madrid ta ci gaba da rike matakin kungiyar da ta fi arziki a duniya da mujallar Forbes ta fitar na shekarar bana.

Duk da Madrid din ta yi rashin kaso biyar cikin dari daga kudaden shigarta wanda ya koma £2.14bn daga shekarar 2014, ta samu kudin shiga da ya kai £489m.

Barcelona ce a matsayi na biyu sai kuma Manchester United a mataki na uku.

Bayern Munich ta kasarJamus ce a matsayi na hudu yayin da Manchester City ke matsayi na biyar, sannan Chelsea wacce ta dauki kofin Premier a bana ke matsayi na shida.

Kulob din Arsenal ne ke matsayi na bakwai a samun kudin shiga, inda Liverpool ke matsayi na takwas, su kuwa Juventus da AC Milan ke mataki na tara dana goma.

Ga jerin kungiyoyin da suka fi samun kudin shiga a duniya

1. Real Madrid $3.26 bn (£2.14bn)

2. Barcelona $3.16 bn (£2.07bn)

3. Manchester United $3.10 bn (£2.03bn)

4. Bayern Munich $2.35bn (£1.5bn)

5. Manchester City $1.38bn (£906m)

6. Chelsea $1.37bn (£899m)

7. Arsenal $1.31bn (£860m)

8. Liverpool $982m (£644m)

9. Juventus $837m (£549m)

10. AC Milan $775m (£509m)

11. Borussia Dortmund $700m (£459m)

12. Paris St-Germain $634bn (£416m)

13. Tottenham $600m (£393m)

14. Schalke 04 $572m (£375m)

15. Inter Milan $439m (£288m)

16. Atletico Madrid $436m (£286m)

17. Napoli $353m (£231m)

18. Newcastle $349m (£229m)

19. West Ham $309m (£202m)

20. Galatasaray $294m (£192m)