An saka kungiyar Aston Villa a kasuwa

Aston Villa Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aston Villa tana mataki na 14 a kan teburin Premier bana

Wasu attajirai karkashin jagorancin tsohon shugaban kasuwancin Chelsea, Paul Smith sun saka Aston Villa a kasuwa.

Ana hasashen cewar kudin da za a sayar da Aston Villa zai kan fan miliyan 150.

Idan aka yi nasarar sayar da kungiyar, watakila Tony Adams ne zai jagoranci harkokin wasan kwallon kafar Villa din.

Smith aminin mai kungiyar Villa ne, Randy Lerner wanda ya saka kungiyar a kasuwa a watan Mayun bara.

Aston Villa mai buga gasar Premier tana mataki na 14 a kan teburi da maki 35, za kuma ta kara da West Ham a Villa Park a ranar Asabar.