Napoli da Dnipro sun tashi kunnen doki

Napoli Dnipro Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Za su buga wasa karo na biyu ranar 14 ga watan Mayu

Napoli da Dnipro Dnipropetrovsk sun tashi wasa 1-1 a gasar cin kofin zakarun Turai wato Europa league da suka buga wasan daf da karshe a Italiya.

Napoli ce ta fara zura kwallo ta hannun Lopez Silva a minti biyar da dawo wa daga hutu, yayin da Dnipro ta farke kwallon ta hannun Seleznyov saura minti 10 a tashi daga wasan.

Daya karawar kuwa da aka yi a Spaniya Sevilla ta lallasa Fiorentina da ci 3-0.

Sevilla ta ci kwallayenta uku ta hannun Vidal Perreu wanda ya zura kwallaye biyu a wasan kafin Gameiro ya kara ta uku saura minti 15 a tashi daga fafatawar.

Dukkan kungiyoyin za su sake karawa karo na biyu ranar Alhamis 14 ga watan Mayu.