Ya kamata Bale ya ci gaba da wasa a Madrid

Bale Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bale ya koma Madrid daga Tottenham a shekarar 2013

Tshohon shugaban Real Madrid Ramon Calderon na fatan Gareth Bale zai ci gaba da murza leda a kulob din a badi.

An yi ta kushe kokarin da Bale ya yi a karawar da Juventus ta doke Madrid 2-1 a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata.

Dan wasan na fama da kalubale a Bernabeu tun lokacin da ya koma kulob din taka leda daga Tottenham kan kudi £85.3m.

Calderon ya shaida wa gidan radiyon Wales cewar bai ga dalilin da dan kwallon ba zai ci gaba da wasa da Madrid ba a badi, domin ya kware a iya taka leda, kuma yana yi da zuciyarsa.

Bale, mai shekaru 25, wanda ya koma Madrid a shekarar 2013, shi ne wanda ya yi karancin taka tamaula da bai wa abokin wasa a Madrid da aka doke su 2-1 a Turin.

Tsohon dan wasan Manchester United Roy Keane ne ya ce Madrid ta buga gasar ne da 'yan wasa 10 a cikin fili, inda ya ce Bale bai yi kuzari ba a karawar.

Eja din Bale Jonathan Barnett ya ce bai kamata a dinga la'akari da fadar albarkacin bakin wasu mutane da ba su san me suke yi ba, sannan suka kasa samun ci gaba a fagen shugabanci ba.

Ramon Calderon ya shugabanci Real Madrid daga shekarar 2006 zuwa 2009.