Sturridge zai koma tamaula a watan Satumba

Hakkin mallakar hoto Daniel Sturridge
Image caption Sturridge na jinya a Amurka

Kocin Liverpool Brendan Rodger ya ce ana saran Daniel Sturridge zai koma murza leda a cikin watan Satumba.

Dan wasan mai shekaru 25, an samu nasara wajen yi masa tiyata a Amurka a makon da ya gabata.

Sau biyu kadai Sturridge ya murza leda tun bayan da ya ji rauni a wasan da Manchester United ta doke su da ci biyu da daya a ranar 22 ga watan Maris.

Rodgers ya ce " Muna saran zai warke zuwa lokacin."

Sturridge ya zura kwallaye 24 a wasanni 33 a kakar wasan da ta wuce amma kuma a kakar wasan bana wasanni 18 kawai ya buga wa Liverpool.