Man City ta mayar da QPR zuwa Championship

QPR Fans
Image caption QPR ce ta 20 a teburin Premier bayan buga wasanni 36

Manchester City ta zazzaga wa QPR kwallaye 6-0 a gasar Premier wasan mako na 36 da suka buga ranar Lahadi a Ettihad.

'Yan wasan da suka ci wa City kwallaye sun hada da Ag├╝ero wanda ya ci guda uku daya daga ciki da bugun fenariti sai Kolarov da Milner da Silva wanda kowannen su ya ci guda-guda.

Da wannan sakamakon QPR ta bar gasar Premier bana a inda za ta koma buga gasar Championship a badi.

Sauran wasanni biyu ya rage a kammala gasar Premier wanda tuni Chelsea ta dauki kofin bana, kuma QPR za ta buga sauran wasannin ne da Newcastle da kuma Leicester.

QPR tana mataki na 20 a teburin Premier bayan buga wasanni 36, kuma sau 7 ta ci wasa ta buga canjaras a wasannin 6 aka doke ta karawa 26 ta zura kwallaye 39 a raga aka zazzaga mata 67 ta kuma hada maki 27 a bana.