"Za mu kai wasan karshe a kofin zakarun Turai"

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ranar Laraba Real Madrid za ta karbi bakuncin Juventus a gasar cin kofin zakarun Turai

Carlo Ancelotti ya ce yana da tabbacin za su kai wasan karshe a kofin Zakarun Turai idan suka murza leda salon wanda suka tashi 2-2 da Valencia a gasar La Liga.

Ranar Laraba Madrid za ta karbi bakuncin Juventus wadda ta doke ta 2-1 a karawar farko da suka yi a Italiya a makon jiya.

Anceloti ya ce za su yi murna idan suka buga salon wasan da suka yi wa Valencia a ranar Asabar, kuma hakan zai sa su kai wasan karshe a gasar.

Ana sa ran Toni Kross zai murmure kafin fafatawar duk da an fitar da shi daga fili a wasan Valencia, yayin da dan kwallon Juventus Paul Pogba zai buga karawar.

Madrid wadda ke rike da kofin zakarun Turai na bara na fatan Karim Benzema zai buga mata wasan bayan da ya yi wata guda yana yin jinya.